A yunwace jama’a suke, ka yi wani abu kafin su yi wani abu, Dino Melaye ga Shugaba Buhari

Sanata Dino Melaye ya yi wata wallafa ta shafin sa na kafar sada zumuntar zamani ta Instagram yana bai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara.

Kamar yadda LIB ta ruwaito, ya bukaci shugaba Buhari ya yi gaggawar tallafa wa mutanen Najeriya sakamakon bakar yunwar da take addabar su.

LIB ta ruwaito yadda Melaye ya yi wallafar a shafin sa inda ya ce:

“Shugaba Buhari, ba lallai ka sani ba, akwai korafi da dama da ake yi a tituna. Mutane su na fama da yunwa, tsadar rayuwa ta na azabtar da talakawa. Ka yi wani abu kafin mutane su yi wani abu.”

“Shugaba Buhari, ba lallai ka sani ba, akwai korafi da dama da ake yi a tituna. Mutane su na fama da yunwa, tsadar rayuwa ta na azabtar da talakawa. Ka yi wani abu kafin mutane su yi wani abu.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *