‘Yan bindiga sun saki karin dalibai 10 da suka sace daga makarantar sakandare ta Bethel Baptist da ke jihar Kaduna.Daliban sun sake samun ‘yanci ne a jiya Asabar, bayan sun shafe kimanin kwanaki 75 a hannun ‘yan binidgar da suka yi garkuwa dasu.
An sace daliban ne dai tun ranar 5 ga watan Yuli lokacin da gungun ‘yan bindiga suka kaiwa makarantar ta Bethel Baptist farmaki a karamar hukumar Chikun da ke Kaduna.
Wani babban jami’I a makarantar ya shaidawa manema labarai cewa an saki daliban ne bayan biyan kudaden fansar da ba a bayyana adadinsu ba.
Karin daliban 10 da suka samu ‘yanci, ya sanya a halin yanzu adadin wadanda ‘yan bindigar suka saki kaiwa 100 daga cikin 121 da suka sace a watan Yuli.
Da fari dai ‘yan bindigar sun saki daliban 28 ne a ranar 25 ga watan Yuli, bayan da aka ce an biya su kudin fansa.