Matasan Sokoto sun kone ‘yan bindiga 13 kurmus har lahira

A Najeriya, wasu Matasa sun kai hari ofishin ‘Yan Sandan dake Tangaza a Jihar Sokoto inda suka kashe mutane 13 da ake zargin cewar ‘Yan bindiga ne, kana suka kona su da wuta.

Bayanai sun ce ‘Yan bindigar na cikin wadanda suka kai hari garin daren Juma’a inda suka kashe mutane biyu da kuma jikkata wasu da dama.

Rahotanni sun ce bayan harin, ‘Yan Sanda da ‘Yan Sakai suka hada kai wajen bin sawun ‘Yan bindigar abinda ya basu damar kama 13 daga cikin su.Labarin tsare Yan bindigar a ofishin ‘Yan Sanda ya harzuka matasan garin, wadanda suka yi gangami wajen kaiwa ofishin hari da kuma kashe wadanda ake zargin, kana suka kona gawarwakin su.

Mai Magana da yawun ‘Yan Sandan Jihar Sanusi Abubakar ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *