Dubban Faransawa sun yi zanga-zanga kan haramta musu farautar gargajiya

Dubban mafarauta sun yi tattaki a Faransa yau Asabar don nuna adawa da hukuncin babbar kotun kasar na haramta farautar tsuntsaye.

Hukumomin Faransar sun ce, akalla mutane dubu 13 ne suka yi zanga-zanga tare da busa kaho a garin Mont-de-Marsan da ke kudu maso yammacin kasar.

A watan Agustan da ya gabata, hukumomin Faransa suka jaddada haramta amfani da dabarun gargajiya wajen farautar tsuntsaye da suka hada da amfani da raga, keji ko kuma tarkon danko, hanyoyin da suka shahara a yankunan kudu maso yammaci da sauran sassan kasar.

Masu fafutuka sun ce tsuntsaye dubu 150 ke mutuwa duk shekara a Faransa, sakamakon dabarun farautar gargajiya da ake amfani da su, a daidai lokacin da yawan tsuntsayen Turai ke raguwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *