Cacar-baka ta yi zafi tsakanin Australia da Faransa kan zargin cin amana

Firaministan Australia Scott Morrison ya yi watsi da zargin da Faransa ta yi musu na yin karya game da soke kwangilar sayo jiragen ruwan kasar ta Faransa.

Firaministan na Australia ya ce sabanin zargin Faransa, tun a watannin da suka gabata, gwamnatin sa ta gabatar da korafi kan yarjejeniyar da suka kulla bayan gano wasu matsaloli daga kirar Faransawan, dan haka ba bin mamaki bane don sun warware ta.

Matakin da Australia ta dauka na rusa yarjejeniyar sayen jiragen yakin ruwan Faransa, inda ta koma ga Amurka, ya fusata Faransawan, abinda ya sanya shugaba Emmanuel Macron ya janye jakadun sa daga Australia da Amurka, wani mataki da ba a taba ganin irinsa ba.

Australia dai ta tsaya kan matsayin ta na cewa babu wata yaudara da ta aikata, yayin da Faransa ke tuhumar ta da cin amana, inda Firaminista Morrison ya dage cewa shi da ministocinsa a baya sun tattauna kan matsalolin da ke tattare da jiragen ruwan yakin na Faransa.

Kalaman Morrison sun zo ne bayan da ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian ya yi amfani da kakkausan harshe wajen sukar Australia, Amurka da Birtaniya.

Le Drian ya caccaki gwamnatin Birtaniya ne kan goyon bayan yaudarar da aka yi wa Faransa, ta hanyar sanya hannu a cikin sabuwar yarjejeniyar cinikin jiragen yakin ruwan da Australia ta kulla da Amurka.

14145 SharesLikeCommentShare

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *