Wani kwararren likita da yayi fice wajen gwajin kwayar halittar Bil Adama a Najeriya yace daga cikin yara 10 da ake gabatar musu domin yin gwaji, 6 daga cikin su ba mutanen da ake zaton iyayen su ne suka haife su ba.
Likitan Abiodun Salami ya kuma bayyana cewar binciken su ya nuna musu cewar akasarin ‘yayan fari ba a gida ake samun su ba.
Salami wanda ya kwashe sama da shekaru 10 yana gudanar da irin wannan binciken kwayar halitta a birnin Lagos, yace wasu mata kan yi mu’amala ta aure tare da wasu mutane kafin samun miji, kuma sau tari koda sun yi aure basa barin irin wannan mu’amalar, saboda ta riga ta zama jiki a gare su.
Salami ya shaidawa Jaridar Premium Times cewar sakamakon wadannan matsaloli ne yanzu haka ya sanya mazaje da dama zuwa asibitocin da suka kware domin gudanar da irin wannan bincike domin gano cewar ‘yayan da suke ikrarin cewar na su ne sun tabbatar nasun ne da kuma kore shakku.
Likitan yace mazaje da dama na yin irin wannan gwajin domin fidda shakku dangane da ’yayan da ake haifa musu a gida, dan kuma tabbatar da sahihancin ‘yayan da ba nasu bane.
Salami yace a baya su kan yi gwaji akalla sau 100 a wata guda, amma kuma yanzu bukatar gwajin ta karu, inda take kaiwa har sau 400 a wata guda.
Likitan yace ana bukatar kwararrun ma’aikata da kuma kayan aiki wajen gudanar da irin wannan gwajin, kuma suna daukar matakan da suka dace wajen kaucewa yin kuskure saboda sun san irin illar dake iya biyo baya.