Yara 5 sun mutu sakamakon fashewar gurneti a yankin Borno

Yara biyar sun mutu sakamakon tarwatsewar wani gurneti a wajen garin Ngala da ke arewa maso gabashin Najeriya, da ke da iyaka da Kamaru.


Jami’an tsaron sa kai da ke yankin sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa lamarin ya auku ne bayan da yaran da ke kiwo suka tsinci gurnetin tare da fara wasa da shi.


Biyu daga cikin yaran biyar sun mutu nan take yayin da sauran ukun suka mutu a wani asibiti da ke garin Mada a cikin Kamaru.


A watan Agustan shekarar 2014, kungiyar mayakan Boko Haram suka kwace Ngala tare da Gamborou, garin da ya kasance cibiyar kasuwanci.


Sojojin Najeriya tare da taimakon na Chadi ne suka kwato garuruwan biyu a cikin watan Satumban shekarar 2015 bayan fafatawar da suka yi tsawon watanni.


Wani mazaunin yankin na Ngala da Gamboru Umar Ari ya shaidawa AFP cewar har yanzu akwai nakiyoyi da bama-baman da basu fashe ba a yankunan karkara kuma yara da dama sun mutu wasu kuma sun jikkata sakamakon wasa da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *