Masu garkuwa da mutane sun sako Kwamishinan watsa labaran Jihar Neja da ke Najeriya kwanaki biyar bayan sace shi da suka yi.
Sakin Kwamishinan na zuwa ne a yayin da daliban makarantar Islamiyyar Salihu Tanko da ke Tegina suka kwashe fiye da kwanaki 75 a hannun ‘yan bindigar kuma ba tare da sakinsu ba duk kuwa da biyan kudi sama da naira miliyan 50 da iyayen yaran suka yi domin a sako ‘ya’yan nasu.
-RFI