Tsohon sakataren gwamnati, Alhaji Ahmad Joda, ya rasu

Tsohon Babban Sakataren Gwamnatin Najeriya lokacin mulkin Soja kuma mutum na farko da Buhari ya ba mukami bayan nasara a 2015 , Alhaji Ahmed Joda, ya mutu.


BBC ta ruwaito daya daga cikin ‘yayan marigayin, Asma’u Joda, ta bayyana cewa mahaifinta ya rsu ne yau Juma’a a Yola, babbar birnin jihar Adamawa.


Alhaji Ahmed Joda ya cika ne yana mai shekaru 91 a duniya.


A cewar DT, Ahmad Joda ya rasu ne bayan jinya a asibitin FMC Yola.


Joda ya yi karatunsa a Najeriya da kuma Birtaniya inda ya halarci Kwalejin Pitmans da ke birnin London daga 1954 zuwa 1956.


Ya rike kujeran sakataren din-din-din lokacin gwamnatin mulkin soja ta Janar Yakubu Gowon (Mai murabus).

Leave a Reply

Your email address will not be published.