Tite mai horar da kungiyar kwallon kafar Brazil ya gayyaci Neymar

Mai horar da kungiyar kwallon kafar Brazil ya gayyaci dan wasan gaban PSG Neymar daga cikin jerryn yan wasa da za su soma atisayi don tunkarar wasanin gasar cin kofin Duniya na Qatar na shekara ta 2022.


Dan wasan Neymar zai buga wasannin da kungiyar Brazil za ta yi nan gaba a kudancin Amurka,wasannin da za a soma farkon watan Satumban shekarar nan ta 2021.


Baya ga dan wasan PSG Neymar,Tite mai horar da kungiyar ta Brazil ya gayyaci Marquinnos dake taka leda a PSG, Thiago Silva daga Chelsea, Casemiro a Real Madrid, Roberto Firmino daga Liverpool da Gabriel Jesus daga Manchester City.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *