Sarkin Musulmi ya bayyana damuwa akan yajin aikin likitoci

Sarkin Musulmin Najeriya Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayyana matukar damuwa akan yajin aikin kungiyar likitocin Najeriya inda ya bukace su da su yiwa Allah su janye domin takaitawa Yan kasa wahalar da suke sha.


Jaridar Daily Trust ta ruwaito sanarwar da Sarkin Musulmin ya gabatar ta hannu Daraktan mulki na Majalisar Koli ta Addinin Musulunci a Najeriya Zubairu Haruna Usman-Ugwu na rokon likitocin da su janye domin bada damar tattaunawa mai muhimmancin tsakanin su da gwamnati.


Sanarwar ta roki likitocin da suyi nazari akan rantsuwar aikin da suka yi da kuma illar da annobar korona keyi a kasa tare da cutar amai da gudawa wajen dakatar da yanzu haka ke hallaka rayuka wajjen janye yajin aikin.


Sarkin Musulmin ya kuma roki ministan kwadago da ya sake tunani akan matsayin gwamnati na dakatar da tattaunawar da suke da likitocin ganin irin illar da Yan Najeriya ke fuskanta.


Sanarwar ta bukaci gwamnatin Najeriya da ta shiga tattaunawa ta gaskiya da shugabannin kungiyar likitocin ta hanyar da zata karfafa guiwa tsakanin bangarorin biyu, inda take cewa gwamnati na da alhakin shawo kan likitocin da kuma duba bukatun su ta hanyar da ta dace.


Sarkin Musulmin ya yabawa saka bakin da Majalisar dokoki tayi tare da wasu Yan Najeriyar da suka nuna damuwar su akan al’amarin, inda ya bukaci ma’aikatar lafiya da na kwadago da kuma likitocin da su koma teburin sasantawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *