Kagame ya cacaki kungiyar Arsenal bayan ta sha kashi hannun Brentford

Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame ya cacaki kungiyar Arsenal jim kadan bayan shan kashin da ta yi a hannun kungiyar Brentford da ci 2-0 a wasan ta na farko na bude gasar Premier ta bana.

Kagame wanda ya dade yana goyan bayan kungiyar Arsenal ya bayyana takaici da irin rawar da kungiyar ta taka a karawar da tayi da Brentford wadda ta shigo gasar Premier bayan kwashe shekaru 74.

Shugaban yace nasarar da Brentford ta samu na doke Arsenal 2-0 ya dace domin ta taka rawa sosai sabanin wadda ‘yan wasan Arsenal suka taka, yayin da ya bayyana cewar wannan wata dama ce da kungiyar zata sake nazari akan abinda ya haifar mata da wannan koma baya.

Kagame yace a matsayin sa na tsohon mai goyawa kungiyar baya, lokacin da ya dace a gudanar da sauyi a cikin ta ya wuce, inda ya bukaci shugabannin kungiyar da su dauki matakin da ya dace.

Shugaban Rwanda ya shaidawa mabiyan sa ta kafar twitter kusan miliyan biyu da rabi cewar, ba zasu amince da gazawa ba, domin ya dace a tsara kungiya yadda zata dinga samun nasara a koda yaushe.

Kagame yace yana da yakinin cewar an san wanda alhakin matsalar kungiyar Arsenal ya rataya a wuyar sa, kuma yana fatar za ayi gyara cikin gaggawa.

Kasar Rwanda na hadin kai da Arsenal wajen tallata harkar yawon bude idon da ake da shi a kasar, kamar yadda aka sanya a rigunan Yan wasan kungiyar da zummar janyo hankalin masu bukatar ziyarar kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *