Gwamnatin Senegal ta rusa kasuwar Sandaga dake Dakar

A Senegal, kwarraru dake kula da harakkokin gine-gine a kasar sun bayyana damuwa tareda nuna bacin ran su biyo bayan rusa kasuwar nan mai dauke da dimbin tarihi mai suna Sandaga dake babban birnin kasar Dakar.


Yan kasuwa daga kasashen ketare da dama ke gudanar da harakokin su na yau da na kullum a wannan kasuwa dake birnin Dakar na kasar Sanegal dake yammacin Afrika.

Rusa wannan kasuwa biyo bayan kulle ta da hukumomin kasar suka yi a shekara ta 2020 ya janyo da dama asara kamar dai yada kungiyoyi a Dakar suka tabbatar.

A cewar kwarraru ,kasuwar  dake dauke da tarihi an gina ta a shekara ta alip 1933 a tsakiyar birnin na Dakar,an kuma rufe kasuwa a shekara ta  2020 da nufin cewa za a kawo gyara, abinda hukumomin kasar suka kaucewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *