Dalibar aji 1 a sakandire ta maka gwamnatin Ekiti a kotu, tana bukatar diyyar N15m

Gift Agenoisa, dalibar JSS1 a makarantar sakandare ta Mary Immaculate dake Ado-Ekiti ta maka gwamnatin jihar Ekiti a gaban babbar kotun jihar tana bukatar gwamnatin ta biyata naira miliyan 15 sakamakon shiga hakkinta na ‘yar adam.


Korafin nata mai lamba HAD/01/CR/2021 wanda Odunayo Agenoisa ya gabatar ga babbar kotun Ado-Ekiti a maimakonta, wanda dalibar tayi ikirarin dakatar da karatunta da gwamnatin tayi ya shiga hakkinta na bil’adama.


Daily Nigerian ta ruwaito cewa, a takardar ta bayyana irin cutarwa da zaluncin da aka mata, akan zuwanta makaranta da wani kitso wanda suke ganin bai dace ba.


A cikin korafinta ta sanya Shugaban makarantar, Mrs Oluwasanmi F.M, kwamishinan ilimin jihar, Dr Olabimpe Aderiye, shugaban malaman jihar da kuma gwamnatin jihar.


A takardar kotun data hada ta bayyana yadda aka kira ta gaban gaba daya daliban makarantar a ranar 22 ga watan Mayu sannan aka yi mata bulalai 20 bisa umarnin shugaban makarantar.


A asalin takardar da lauyanta, Mr Timmy Omotoso ya gabatar, ya kawo dokoki kwarara na 1,3,4,5 da 6 na hakkin bil’adama na 2009 wadanda sashi na 315 suka gabatar daga kundin tsarin mulkin 1999, ta bukaci naira miliyan 15 akan dakatar da karatunta da sukayi.


Ta bukaci a yi gaggawar mayar da ita makaranta don ta cigaba da karatunta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *