Canada ta soma kwashe mutane daga Afghanistan

Gwamnatin Canada ta sanar da shirin ta na karbar yan gudun hijira daga Afghanistan dubu 20 a wani tsari da gwamnatin kasar ta shifuda ganin matsakaicin yanayi da mutan kasar suka fada.


Ministan shige da fice na Canada ya bayyana cewa babu ta yada Canada za ta rufe idanu gani matsallolin da jama’a suka fada a kasar ta Afghanistan.

Jirgin farko dauke da yan kasar ta Afghanistan ya sauka filin tashi da saukar jirage na birnin Toronto na kasar ta Canada dauke da wasu daga cikin tsofin ma’aikata yan kasar Afghanistan da suka yi aiki da Canada a baya.

Fadar Firaministan kasar ta Canada ta ce ta na bi sau da kafa yada lamura ke tafiya a kasar ta Afghanistan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *