Doyin Okupe, tsohon babban hadimin tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya ce jam’iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC) da jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) duk daya ce.
A cewar dan siyasa, babu abin da ya raba jam’iyyun siyasar Najeriya guda biyu saboda kashi saba’in na mutanen da ke rike da madafun iko a APC a yau dukkansu ‘yan PDP ne.
Mista Okupe ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, 13 ga watan Agusta, lokacin da ya fito a wani shirin ARISE News na The Morning Show.
Ya ambaci gwamnan Ogun mai ci da tsoffin gwamnonin jihar a matsayin mambobin da suka rike madafun iko a PDP amma yanzu suka tsinci kansu a matsayin jagorori a APC.
“Maganar gaskiya ita ce, da kyar in akwai wani banbanci tsakanin jam’iyyun siyasar biyu. A bayyane yake. Idan yau ina PDP kuma gobe ina APC toh ba mutum daya ba ne …
“Kashi hamsin cikin dari na wadanda ke rike da madafun iko a APC a yau, in ba 70% ba, duk mutanen PDP ne.”
Ya kuma ce gaba daya hayaniyar jami’an kasa da suka yi murabus daga PDP, da kuma rikicin da APC ke fama da shi, kawai yunkuri ne zuwa zaben 2023.
A baya, tsohon shugaban hukumar INEC, farfesa Attahiru jega ya gargadi ‘yan Najeriya kan sake zaban shugabanni daga jam’iyyun APC da PDP.
A cewarsa, wadannan jam’iyya dukkansu hali daya suke tafe akai, kuma babu abinda suka taba wa ‘yan Najeriya tsawon shekaru 20 da suka yi suna mulki.