Ana sa ran Shugaba Buhari zai dawo Najeriya a yau

Ana sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai dawo Najeriya da karfe 5:00 na yammacin yau Juma’a, 13 ga watan Agusta, bayan kimanin makonni biyu a kasar Ingila.


Jaridar Nigerian Tribune ta rahoto cewa tuni aka shirya hukumomin tsaro a babban birnin tarayya domin dawowar shugaban.


Shugaban kasar dai ya yi tafiyar ne don halartar taron Ilimi na Duniya kafin ya tsaya domin duba lafiyarsa.
A gefe guda, mun ji cewa mai girma shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyara da kansa zuwa gidan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a Landan, kasar Ingila.


Mai taimaka wa shugaban Najeriya a kafofin sadarwa na zamani, Bashir Ahmaad ya fitar da hotunan wannan gana wa da aka yi tsakanin manyan kasar.


Kamar yadda mu ka samu labari, Muhammadu Buhari ya ziyarci tsohon gwamnan Legas, Bola Ahmed Tinubu ne a ranar Alhamis, 12 ga watan Agusta, 2021.

Leave a Reply

Your email address will not be published.