Hatsarin mota ya kashe mutum 11 a Jihar Osun

Hukumar kiyaye haɗura reshehn jihar Osun a Najeriya ta ce mutum 11 sun rasu sakamakon mummunan hatsarin mota da ya faru a Gbangan.

Mai magana da yawun hukumar, Agnes Ogungbemi, ita ce ta bayyana hakan ga manema labarai a garin Osogbo, a cewar rahoton kamfanin labarai na NAN.

Ogungbemi ta ce hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:21 na daren Juma’a a kusa da sakatariyar Ƙaramar Hukumar Ayedaade.

Ta ƙara da cewa wasu motoci ne guda biyu suka yi karo da juna.

“Mutanen da hatsarin ya ritsa da su sun haɗa da maza 30 da mata biyu da kuma yarinya ɗaya,” in ji ta.

“Maza 11 ne suka rasu nan take yayin da sauran 22 ɗin suka ji raunuka daban-daban, inda kuma aka garzaya da su asibiti.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *