’Yan Bindiga Sun Yi Barazanar Kashe Ragowar Daliban Jami’ar Greenfield

’Yan bindigar da suka yi garkuwa da daliban Jami’ar Greenfield dake Kaduna sun yi barazanar kashe ragowar daliban makarantar guda 17.

Dalibai 22 da wani ma’aikacin jami’ar guda daya ne dai aka kwashe daga makarantar wacce take kan hanyar Kaduna zuwa Abuja ranar 20 ga watan Afrilun 2021, kafin daga bisani a kashe biyar daga cikinsu a cikin mako daya.

Hakan dai na kunshe ne a cikin wata tattaunawa da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA), da jagoran ’yan bindigar wanda ya bayyana sunansa da Sani Idris Jalingo ranar Litinin.

Sani ya ce muddin Gwamnatin Kaduna ko iyalan daliban suka gaza biyan su Naira miliyan 100 a matsayin kudin fansa da kuma basu sabbin babura kirar Honda nan da ranar Talata, to babu makawa za su kashe ragowar mutanen.

Ya ce yanzu haka akwai dalibai 17 a hannunsu, mata 15 da maza biyu, ciki har da wani jikan Sarkin Zazzau na 18, marigayi Shehu Idris wanda ya ce sunansa Hamza.

’Yan bindigar dai sun ce iyalan daliban sun tara Naira miliyan 55 sannan suka aika musu da su, amma ya ce sun kashe kudaden wajen ciyar da daliban.

Ya lashi takobin cewa wannan shine gargadinsu na karshe wanda matukar gwamnati ko iyalansu suka ki kawo kudin to za su kashe su baki daya.

“Mun ji dukkan kalaman Gwamnan Kaduna cewa ba zai biya kudin fansa gare mu ba saboda kada mu kara sayen makamai.

“Ina mai tabbatar maka da cewa matukar aka gaza bamu Naira miliyan 100 da babura kirar Honda wanda aka fi sani da Boko Haram guda 10 nan da ranar Talata, to sai dai a zo da motoci a kwashi gawarwakinsu,” inji jagoran ’yan bindigan.

Da aka tambaye shi ko yana ganin abinda suke yi a matsayin ta’addanci sai ya ce shi ba dan ta’adda ba ne, neman abinci yake.

Ya kuma shawarci jami’an tsaro da kada su bata lokacinsu waurin kokarin bin sahunsu, inda ya ce yaransa ba sa shiga manyan garuruwa, saboda haka kama su zai yi matukar wahala.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *