Tamowa: Yara 81 Sun Rasu, 5,200 Na Asibiti A Nasarawa

Kananan yara akalla 81 sun rasu daga cikin yara 5,200 da cutar tamowa ta rashin abinci mai gina jiki ta kwantar a asibitoci a Jihar Nasarawa.

Hakan na faruwa ne a cikin wata takwas da suka gabata a kananan hukumomi 13 na Jihar Nasarawa, a cewar Babbar Jami’ar kula da abinci mai gina jiki ta Jihar, Halima Yusuf.

Halima Yusuf ta shaida wa taron wayar da kai kan abinci mai gina jiki cewa “Kananan yara 81 sun rasu daga cikin yaran da aka kwantar a asibitoci a jihar, wasu 2,000 kuma sun murmure.”

Shugaban Kwamitin Abinci Mai Gina Jiki na Jihar, Osama Abdul, ya ce kwamitin ya bullo da hanyoyin magance matsalar rashin abinci mai gina jiki, wadanda ake sa ran kashe wa Naira biliyan uku.

Tun da farko Babbar Sakataren kungiyar samar da abinci mai gina jiki a a Najeriya CS-SUNN, Beatrice Eluaka, ta bayyana damuwa game da yawaitar matsalar karancin abinci mai gina jiki a jihar ta Nasarawa.

Ta jaddada muhimmancin Gwamnatin Jihar ta bullo da hanyoyi na cikin gida domin magance matsalar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *