NDLEA Ta Sanar Da Fara Kai Farmaki Dakunan Hada Muggan Kwayoyi

Shugaban hukuamar NDLEA Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya) ya kare farmakin da hukumar take kai wa dakuna hada muggan kwayoyi da kuma filayen gonakin da ake shuka tabar wiwi a fadin kasar nan.

Janar Marwa ya bayyana haka ne a mukalar da ya gabatar na tsarin da Nijeriya ta yi a kan yaki da safara da kuma hada miyagun kwayoyi a yanzu da kuma nan gaba, a taron da aka yi a garin Bienna ta kasar Austria.

Ya dauki wannan matakin ne don safara da shaye shayen kwayoyi yana barazana ga harkar tabbatar da tsaro a fadin kasar nan.

Bayanin haka ya na kunshe ne a takardar sanarwa da jami’in watsa labarai na hukumar, Mr Femi Babafemi, ya sanya wa hannun aka kuma raba wa manema labarai a garin Abuja ranar Juma’a, ya kuma ce, masu safarar kwayoyin sun mayar da Nijeriya kamar wata hanya na zirga zirga da muggan kwayoyin.

“Yanzu abin ya kuma kara lamari don kuwa an sami yanayin a aka hadawa tare da shan kwayoyin duk a cikin gida Nijeriya.

“Kwayoyin da ake safarar sun hada da tabar wiwi da cocaine, heroin da kuma psychotropic haka kuma ana safara methamphetamine da tramadol.

“NDLEA ta samu nasarar lalata manyan gonakin taba wiwi da kuma dakuna hada muggan kwayoyi a fadin tarayyar kasar nan a yan shekarun nan,” inji shi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *