Kungiyar Gwamnonin Nijeriya Ta Bukaci Ma’aikatan Kotu Su Janye Yajin Aiki

Kungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) da Taron Shugabannin Majalisun Jihohi, sun yi kira ga ma’aikatan shari’a da ke yajin aiki da su dakatar da yajin aikin da suke yi, domin amfanin kasar.

Gwamna Aminu Tambuwal na Jihar Sakkwato, wanda kuma shi ne Mataimakin Shugaban kungiyar ta NGF, shine ya yi wannan rokon a lokacin da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai na fadar Gwamnatin, bayan ya jagoranci jami’an taron shugabannin majalisun jihohi zuwa ofishin Shugaban Ma’aikata ga Shugaban Kasa.

“Yanzu haka mun gama tattaunawa da Shugabannin Majalisar, manyan Alkalai na Jiha, da bangaren shari’a, don ci gaba da aiki, har ila yau kuma Ministan Kwadagon da kuma sauran kungiyoyin da ke yajin aikin don yin wannan kira a gare su, kuma ya yaba da hakan yana mai cewa muna samun ci gaba.

Tambuwal ya kara da cewa: “Tun daga farko, a lokacin Majalisar ta 8, karkashin jagorancin Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki da Shugaban Majalisar Dogara, NGF karkashin Abdulaziz Yari a lokacin, sun gana da su kuma sun goyi bayan ikon cin gashin kai ga majalisun dokokin jihar da bangaren shari’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *