Shugaban Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati a Najeriya EFCC, Abdulrasheed Bawa ya ce zai sauka daga mukamunsa idan wani ya nemi ya yi wani abin da ya saba ka’idar aikins shi.
Ya kuma kara jaddada dokar da ta bai wa EFCC damar binciken kadarorin ma’aikatan banki.
Bawa ya fara bayyana wannan ra’ayin nasa ne lokacin da ya yi wata tattaunawa da gidan talabijin na kasar NTA.
An raba wa ‘yan jarida rubutaccen bayanin shugaban ta hannun shugaban masu yada labarai na hukumar Mista Wilson Uwujaren.
Yace zai kasance mai tsoron Allah da bin ka’idojin da doka ta tanada.
Yace “Zan ci gaba da aiki domin yin abin da ya kamata. wannan hukuma karkashin kulawata za ta zama mai bin doka da oda.
“Idan wani ya nemi in yi abin da ya ci karo da ka’idar aiki na ko abin da doka ta tanada, zan ajiye wannan aikin ne kawai”.