Kotu ta ɗaure Farfesa a Akwa Ibom kan maguɗin zaɓe

Wata babbar kotu a jihar Akwa Ibom da ke kudu maso kudancin Najeriya ta aike da wani Farfesa masanin kimiyyar kasa a Jami’ar Calabar, Peter Ogban, gidan yari na tsawon shekara uku kan zargin magudin sakamakon zabe.

Ogban shi ne baturen zabe a mazabar Arewa maso Yammaci Akwa Ibom a zaben 2019.

Ana kuma zargin shi da wallafa labarai da kuma sanar da sakamakon karya a kananan hukumomin Oruk Anam da Etim Ekpo.

Hukumar zabe ce ta gurfanar da shi a gaban babbar kotun jihar da ke Ikot Ekpene.

An same shi da laifin sauya sakamakon zaben domin taimakawa jam’iyyar APC mai mulki da tankware jam’iyyar PDP ta hamayya.

A wani zama da akai yi, Farfesan ya shaida wa kotu yadda aka sauya sakamakon zaben ta yadda APC za ta samu nasara kan PDP.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *