Koriya ta Arewa na barazana ga zaman lafiyar duniya

Koriya ta Arewa ta harba wasu makamai masu linzami da suka sauka a tekun Japan bayan shafe daruruwan kilomita.

Firaministan Japan Suga Yoshihide ya kira lamarin a matsayin barazana ga zaman lafiya da keta ka’idojin Majalisar Dinkin Duniya.

Kwamitin tsaron kasa na Koriya ta Kudu na gab da zama domin tattauna lamarin.

Wannan ne gwajin makami mai linzami na farko da Koriya ta Arewa ta yi tun bayan da shugaba Joe Biden ya kama mulki a watan Janairu.

A makon da ya gabata, manyan jami’an gwamnatin Amurka sun ziyarci jami’an gwamnatin Japan da Koriya ta Kudu inda suka bayyana bukatar kawo karshen shirin Nukiliyar Koriya Ta Arewa abin da Koriya ta Arewan ta bayyana a matsayin magana maras tushe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *