An hana buɗa-baki a masallacin Makka a lokacin azumi

Hukumomi a Saudiyya sun ce ba za a rika yin buɗa-baki ba a masallacin maka a lokacin azumi.

Hakan kuma ya shafi sahur da ake yi cikin jama’a a gidajen cin abinci da otel-otel, lokacin azumin na Ramadana.

Wannan mataki na zuwa ne bayan wata tattauna wa da hukumomin kasar suka yi kan matakan da za a dauka domin kare kai da kuma mutane daga kamuwa da wannan cuta ta korona a yayin azumi da kuma bikin sallah.

Bayan amince da wasu ma’aikatu shida suka yi da wannan mataki ne ya sa aka sanar da shi, domin duk masu aikin ibada a lokacin azumin suka kwana da sanin haka.

Ma’aikatar kula da al’amuran cikin gida ta kasar ta ce ta haramta shan ruwa da sahur a otel, ta kuma haramta taruwar mutane da yawa a wuraren shakatawa, sannan za a kulle kananan wuraren shakatawar,a kuma samar da masu sanya idanu kan tabbatar da cewa ana aiki da wadannan dokoki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *