An gano abin da ya kashe sama da giwaye 330 a Botswana

Hukumomin muhalli a Botswana sun ce sun kara gano gawawakin sama da giwaye 39 tun daga watan Janairu, a ci gaba da binciken da suke yi kan yawatar mutuwar giwayen da ake samu a kasar.

Wannan karin da aka samu na mutuwar giwayen a Moremi ya sa adadin giwayen da suka mutu ya kai 330, tun daga watan Mayun bara zuwa Yuni kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Ma’aikatar muhallin ta ce daga wani bincike da ta gudanar ta gano cewa wata cuta ce da ke kama dabbobi ce ke janyo mutuwar dabbobin.

Sai dai har yanzu ba a kai ga gano dalilin mutuwar wasu namun dawan a cikin dazukan kasar.

A bara an ta yada cewa wata cuta ce da dabbobin ke dauka a ruwan da suke sha ke janyo mutuwar ta su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *