Sama da mutum dubu uku korona ta kashe a rana guda a Amurka

Sama da mutum dubu 3 sun mutu sakamakon annobar korona a cikin sa’o’i 24 da suka gabata a Amurka – adadi mafi yawa da aka taɓa gani a rana guda kawo yanzu a duniya.

Ana cigaba da samun ƙaruwar sabbin mutane da ke kamuwa da cutar a Amurka, sannan asibitoci na cika a sassan ƙasar, musamman a California inda aka samu ƙaruwar mutane da ake kwantarwa da sama da kashi 75 cikin 100 a cikin makwanni biyu da suka gabata.

Ƙwararu a fanin lafiya sun ce muddin mutane suka ci gaba da bijirewa gargaɗi da tafiye-tafiye mara kan gado da taruka to annobar za ta cigaba da bazuwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *