Maina ya yanke jiki ya faɗi a kotu

Tsohon shugaban kwamitin yi wa tsarin fansho na Najeriya garambawul, Abdulrasheed Maina ya yanke jiki ya faɗi a kotu a yayin da ake sauraren ƙara kan tuhumarsa da ake yi kan almubazarancin dala biliyan biyu.

Wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna Maina ya yi zaman zauna ka ci doya yayin da ake riƙe da shi bayan ya farfaɗo.

A kwanakin baya ne dai aka kama Maina a Jamhuriyyar Nijar inda ‘yan sandan ƙasa da ƙasa suka tasa ƙeyarsa zuwa Najeriya domin ci gaba da shari’arsa bayan ya tsere daga belinsa da aka bayar a kwanakin baya.

Hukumar EFCC ce ke ƙarar Maina kan tuhume-tuhume 12, daga ciki har da mallakar manyan kadarori a Abuja babban birnin Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *