Covid-19: El-Rufai ya yi barazanar sake saka dokar kulle a Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya yi barazanar sake saka dokar kulle a jihar sakamakon ƙaruwar annobar korona.

A wata tattaunawa da manema labarai ɗaya daga cikin masu taimaka wa gwamnan kan kafofin watsa labarai, Abdallah Yunus Abdallah, ya bayyana cewa haƙƙi ne na gwamnan ya kare dukiyoyi da rayukan al’ummar jihar Kaduna, shi ya sa ya yi wannan gargaɗin.

Ya kuma jaddada aniyar gwamnan na saka dokar kullen idan mutane suka ƙi bin ƙa’idoji da kuma idan aka ci gaba da samun ƙaruwar adadin masu kamuwa da cutar.

Ko a jiya Laraba sai da gwamnan ya bayar da rahoton cewa mutum 64 sun kamu da cutar a jihar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *