Zaben Kananan Hukumomi: Rikici Ya Barke A Jam’iyyar APC Reshen Kano

Wata kungiyar mambobin jam’iyyar APC a jihar Kano karkashin jagorancin Hussaini Isa Mairiga sun yi kira ga Babban Ofishin jam’iyyar na kasa da ya kafa kwamiti na rikon kwarya da zai jagoranci jam’iyyar a jihar.

A wata tattauna wa da ya yi da manema labarai, Mairiga ya zargi Shugaban jam’iyyar na jihar Kano, Abdullahi Abbas, da rashin iya shugabanci kuma ya gaza dinke barakar jam’iyyar.

Mairiga wanda ya ce yana magana ne da yawun kungiyar Legacy Group; mambobin rusasshiyar ANPP, CPC da ANC, tun a 2014 kafin gudanar da zaben 2015 ya zargin Abdullahi Abbas da rashin iya shugabanci, wanda ya sabawa doka da oda wanda a cewarsa dukkanin abin da ya sabawa ra’ayinsu to bashi da amfani.

Mairiga ya kara jan hankalin ‘yan takarar kananan hukumomin da za su fafata a zaben da za a gudanar a watan Janairun 2021a kan muddin suka bi tsarin Abdullahi Abbas to kuwa tabbas sun yi a banza.

Mairiga, wanda tsohon mataimaki na musamman ne ga Sanata Ibrahim Shekarau a lokacin da yake gwamnan jihar Kano, ya yi kira ga Babban Ofishin jam’iyyar APC da ke Abuja da ya samar da wani shugaban rikon kwarya wanda a cewarsa rashin yin hakan ka iya haifar da rugujewar jam’iyyar a 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *