‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 1, Sun Yi Garkuwa Da 5 A Neja

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe mutum guda tare da yin garkuwa da wasu mutanen biyar a garin Bwari- Sabo da ke karamar hukumar Tafa dake jihar Neja.

Wani mazaunin yankin mai suna Shu’aibu ya ce ‘yan bindigar sun mamaye garin ne da misalin karfe 12 na dare, inda suka harbe wani mazaunin yankin da ya yi yunkurin tserewa.

A cewarsa, masu garkuwar sun kai hari kan wasu gidaje uku, inda suka kashe mutum daya sannan suka yi awon gaba da mutum biyar zuwa cikin daji.

Shugaban Karamar Hukumar ta Tafa, Ibrahim Mami Ijah, ya tabbatar da faruwar harin, duk da yake bai yi cikakken bayani kan lamarin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.