Shirme Ne Kiran Buhari Ya Yi Murabus —Gwamnatin Tarayya

Gwamantin Tarayya ta ce kiraye-kirayen neman Shugaba Buhari ya yi murabus daga matsayinsa alama ce ta rashin sanin ya-kamata.

Ministan Yada Labarai, Kai Mohammed ya bayyana haka a lokacin ganawarsa da Kungiyar Masu Gidajen Jarida ta Najeriya (NPAN).

Ministan ya ce neman Shugaba Buhari ya yi murabus saboda lalacewar sha’anin tsaro “shigar kazamar siyasa ce cikin al’amarin tsaro”.https://c2c185254ee9a5e8b8798311cc7866ab.safeframe.googlesyndication.com/safeframe/1-0-37/html/container.html

A farkon makon nan ne Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta bukaci Buhari ya yi murabus bayan harin kungiyar Boko Haram da ta kashe manoma 43 a Zabarmari, Jihar Borno.

NEF ta zargi Buhari da rashin katabus wurin kawo karshen matsalar tsaro da kashe-kashe da suka addabi yankin Arewa.

“A kasashen da suka waye, duk shugaban da ya kasa samar da tsaro, sauka yake yi daga mukaminsa”, inji kakakin NEF, Hakeem Baba-Ahmed.

Ita ma kungiyar yankin Neja Delta (PANDEF) da Gamayyar Dattawan Najeriya kan Zaman Lafiya da Kyakyyawan Shugabanci (CONEPAGG) sun bayyana takaici kan tabarbarewar sha’anin tsaro a Najeriya.

Kiraye-kirayen babu fa’ida

Da yake magana kan harin Zabarmari da Boko Haram ta kashe sama da manoma 43, Lai Mohammed ya ce, “Bayan harin an yi ta neman Shugaban Kasa ya sauka daga mukaminsa.

“Wannan mummunan salo ne na sanya siyasa a sha’anin tsaro wanda babu dattaku a ciki.

“A 2015 an zabi Shugaban Kasa a wa’adi mai shekara hudu sannan a 2019 aka kara zaben shi a wani wa’adi na shekara hudu. Babu kiraye-kirayen da za su hana shi kammala wa’adinsa”, inji ministan.

Lai Mohammed ya ce gabanin mulkin Buhari Boko Haram na kai-komo da kai hare-hare yadda ta ga dama a garuruwan Arewa kamar Kano, Kaduna da Jos da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.