Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Wa Maryam Sanda Hukuncin Kisa

Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta tabbatar da hukuncin kisa da Babbar Kotun Birnin Tarayya ta yanke a kan Maryam Sanda bayan an tuhume ta da kashe mijinta.

Alkalan Kotun uku ne suka ayyana wannan hukunci ranar Juma’a bayan sun yi watsi da daukaka karar da Maryam ta yi.

A watan Janairu ne dai aka tuhume ta da kashe mijinta, Bilyaminu Bello, wanda da ne a wajen tsohon minista kuma tsohon shugaban jam;iyyar PDP, Haliru Bello.

Lauyoyinta sun ce za su daukaka kara zuwa Kotun Koli.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *