Zabaɓɓen shugaban Amurka mai jran gado Joe Biden, ya bayyana cewar zai buƙaci Amurkawa su sanya takunkumi a kwanaki dari na farkon gwamnatinsa don hana yaɗuwar annobar korona a fadin ƙsar.
Ya ce ko tantama babu, za a samu raguwar masu kamuwa da cutar idan jama’a suka amsa kiran.
Ya ce zai yi odar takunkuman da ma’aikata za su riƙa amfani da su a dukkanin gine-ginen gwamnati, kama daga kan ma’aikatu da sauran hukumomi.
Zuwa yanzu an samu masu cutar miliyan 14 a Amurka, yayin da yawan wadanda suka mutu ya tasamma 300,000.
Ya ce yana fatan cewa za a samu raguwar mutanen da ke kamuwa kwarai da gaske, musamman tunda zuwa lokacin an fara yiwa jama’a rigakafi.
Masana kundin tsarin mulki a Amurka dai sun ce shugaban ƙasar bashi da ikon tursasawa jama’a sanya takunkumi, amma Mista Biden ya bayyana cewa shi da mataimakiyarsa Kamala Harris za su yi jagoranci abin koyi, ta hanyar sanya takunkumi a ko da yaushe.
Zaɓaɓɓen shugaban ya bayyana cewa ya nemi kwararran jami’in yaƙi da cutuka masu yaɗuwa na ƙasar Dakta Anthony Fauchi ya ci gaba da kasancewa a matsayin mai ba gwamnatinsa shawara a kan yaƙi da annobar.
Ya ce ci gaba da kasancewa da shi zai ƙara sanya wa jama’a ƙarfin guiwar cewa da gaske gwamnatinsa ta ke, a ƙudurinta na yaƙi da cutar korona.