Shekarau Ya Kalubalanci Buhari Kan Kin Sauke Manyan Hafsoshin Tsaro

Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya a zauren Majalisar Dattawa, Ibrahim Shekarau, ya kalubalanci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan kin sallamar Manyan Hafsoshin Tsaro duk da yadda matsalar tsaro ke ci gaba ba tabarbarewa a kasar.

Shekarau ya bayyana haka ne a ranar Alhamis cikin shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels.

Sanatan wanda kuma tsohon gwamnan jihar Kano ne ya ce hawa kujerar nakin da Shugaba Buhari ya yi kan sallamar Manyan Hafsoshin Tsaron kasar ya saba wa doka da kundin dokokin kasa.

Kiran nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da sabunta kiraye-kirayen sallamar manyan hasfoshin tsaro biyo bayan kisan gillar da mayakan Boko Haram suka yi wa manoma a kauyen Zabarmari na jihar Borno.

Sanata Shekarau ya ce manyan hafsoshin tsaron sun gaza sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na tabbatar da tsaron kasa.

A cewarsa, bisa kundin kundin dokokin Najeriya, manyan hafsoshin tsaron sun zarce lokacin da ya kamata su yi a matsayin ma’aikatan gwamnati, saboda haka tuburewar da Shugaba Buhari ya yi na kin sallamarsu ya ci karo da dokokin kasar.

Ya ce, “Buhari yana ci gaba da karya doka, saboda doka ta ce duk wanda ya kai shekaru 35 yana aiki ko ya kai shekaru 60 da haihuwa dole ya ajiye aiki babu makawa.”

“Ba ma maganar gazawarsu kawai ake ba, manyan hafsoshin tsaron ba ma’aikatan Buhari bane, ma’aikata ne na gwamnatin tarayya kuma an yi tanadin doka ga dukkan ma’aikatan gwamnati.

“Ko da Shugaban Kasa yana ganin suna da wata riba ko amfani a garesa, dole ne ya bari su yi ritaya kamar yadda doka ta tanada ga kowane ma’aikacin gwamnati da ya kai munzalin ajiye aiki, idan ya so yana iya daukarsu aiki a matsayin ministoci, ko mashawarta,” inji Shekarau.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *