Tsohon mataimakin gwamnan Zamfara, Wakkala, ya sauya sheka daga APC zuwa PDP

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Ibrahim Wakkala, ya sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP).

Wakkala ya bayyana hakan ranar Laraba yayin hira da manema labarai a Gusau, birnin jihar Zamfara, Channels TV ta ruwaito.

Ya kasance mataimakin gwamnatin jihar lokacin mulkin tsohon gwamna AbdulAziz Yari.

Yayin bayani kan dalilinsa na sauya sheka, Wakkala ya ce tun lokacin da APC ta rasa mulki a 2019, an daina tuntubarsa kan abubuwan dake gudana a jam’iyyar.

Ya ce tun lokacin da gwamna Bello Matawalle ya hau mulki, ya kasance mai bashi shawara, musamman wajen magance matsalolin tsaro a jihar.

Ya kara da cewa ya rubuta wasika na musamman ga tsohon maigidansa, AbdulAziz Yari, kan shawarar da ya yanke na fita daga APC.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *