An Cafke Uwar Da Ta Sayar Da Jaririyarta ‘Yar Watanni 4 A Katsina

Rundunar ’Yan sanda a jihar  Katsina ta cafke wata uwa mai sana’ar karuwanci da ake zargi da sayar da jaririyarta ’yar watanni hudu da haihuwa.

Mai Magana da yawun rundunar, SP Isah Gambo ne ya tabbatar da faruwan hakan yayin zanta wa da Aminiya a ranar Litinin.

SP Gambo ya ce an kama wadda ake zargi mai shekaru 25, Zainab Adamu wadda aka fi sani da inkiyar Justina, inda ta hada baki da wata kawarta, Ruth Kenneth wajen sayar da jaririyarta a kan naira dubu 300.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *