Gwamna El-Rufai na jihar Kaduna ya bayyana damuwarsa a kan rashin tsaron da ke addabar jiharsa – A cewarsa, ‘yan sandan da yakamata a ce suna yakar ‘yan ta’adda suna can suna rike jakunkunan manyan mata.
Gwamnan wanda ya bayyana haka a wani shirin gidan talabijin ya kuma bayyana bukatar da ke akwai na canja kundin tsarin mulkin Najeriya domin bai wa jihohi damar amfana da ‘yan sandansu, inda ya nuna takaicinsa a kan kashe-kashen da ake yi a jiharsa, tare da bukatar ‘yan sanda su tashi tsaye don fuskantar lamarin.
Gwamnan ya ce ya kamata a ce gwamnonin jihohi ne suke da alhakin kulawa da ayyukan yau da kullum na ‘yan sandan jihohinsu.