An kama Abdulrasheed Maina a Nijar

Rahotanni daga Jamhuriyyar Nijar na cewa wasu jami’an tattara bayanan sirri sun damƙe Abdulrasheed Maina a daren ranar Litinin.

Kafar watsa labarai ta PR Nigeria ta ruwaito cewa wani babban jami’in tattara bayanan sirri ya shaida mata cewa an samu nasarar kama Maina ne sakamakon irin danƙon zumuncin da kuma yarjejeniya ta tsaro da ke tsakanin Najeriya da Nijar.

Abdulrasheed Maina, wanda tsohon shugaba ne a kwamitin yi wa tsarin fansho na Najeriya garambawul, na fuskantar tuhume-tuhume har guda 12 tare da wani kamfani, inda hukumar EFCC ce ta gabatar da tuhume-tuhumen a kansu.

EFCC na zargin Maina da amfani da asusun wani kamfani wajen halatta kuɗin haram har kusan naira biliyan biyu, wanda cikin kuɗin ne ake zargin ya sayi wasu kadarori a Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published.