Alkaluman wadanda suka rasu a Zabarmari sun karu zuwa 78.

Tawagar hadin gwuiwa ta sojoji da fararen
hula sun sake gano karin akalla gawarwaki 35
da suka fara kumbura a yankin Zabarmari da
ke karamar hukumar Jere a jihar Borno.


Sabbin gawarwakin 35, wadanda aka gano a
ranar Litinin, daban su ke da 43 da aka yi
jana’izarsu, hakan ya sauya alkaluman
mutanen da aka tabbatar an kashe zuwa
mutum 78.


An fara tsara neman gawarwakin sauran
mutanen a ranar Lahadi amma sai hakan ba ta
samu ba.


Tawagar da ta gano gawarwakin ta binnesu
nan take saboda ba za’a iya motsa su daga
wuraren da suka fara rubewa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *