‘Yan Najeriya na Allah-wadai da kalaman Garba Shehu

‘Yan Najeriya, a shafukan sada zumunta, na yin Allah-wadai da kalaman Garba Shehu mai magana da yawun Shugaba Buhari game da kalaman da ya yi a hirarsa da sashen Ingilishi na BBC a safiyar Litinin.

Kakakin shugaban ƙasar na amsa tambaya ne kan ko manoma 43 da ake zargin Boko Haram da yi wa yankan rago a Borno sun samu amincewar jami’an tsaro kafin su yi noma a gonakin nasu.

Sai ya amsa da cewa: “A’a, wajibi ne a faɗi gaskiya. Shin sojoji da ke kula da yankin sun amince? Ko wani daga cikinsu ya nemi amincewa kafin ya ci gaba da aiki? Shugabannin sojoji sun faɗa mani cewa ba su nemi shawara ba, saboda haka wannan damar ‘yan ta’addan suka yi amfani da ita.”

Garba Shehu ya ƙara da cewa akasarin yankunan an ƙwace su ne daga hannun Boko Haram kuma akwai wurare da yawa da ba a amince mazaunansa su koma ba tukunna. “Ya kamata a ce sojoji sun amince tukunna kafin a ci gaba da ayyuka a yankunan.”

Mutane da dama a Twitter sun caccake shi kan waɗannan kalamai nasa, ciki har da waɗanda suka yi masa fatan ya mutu ta wannan hanya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.