Kisan Manoma: Dabararka Ta Gaza —Majalisa Ga Buhari

Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Enyinnaya Abaribe, ya ce yanzu lokaci ya yi na gwamnati ta dauki tsauraran matakai tare da yin nazarin dabarunta tunda na yanzu sun gaza matuka.

Kwamitin ya kuma nuna alhini tare da bacin rai game da kisan da aka yi wa manoman shinkafa a Jihar Borno.

Sanarwar kwamitin ta kara da cewa abun takaici ne a ce lokacin da ake sa ran yin girbin kayan abinci ya koma lokacin zaman makoki.

Sun kuma aike da sakon ta’aziyya ga gwamnatin Borno da iyalan wanda aka yi wa kisan gillar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *