Amurka ta yi Allah-wadai da kisan manoma 43 a Borno

Amurka ta yi Allah-wadai tare da nuna ɓacin ranta game da kashe manoma 43 da ake zargin ƙungiyar Boko Haram da aikatawa ranar Asabar a Zabarmari na Jihar Borno.

Wata sanarwa da ofishin jakadancin Amurkar ya fitar a yau Litinin ta bayyana kisan a matsayin “babbar alama” ta abin da ya sa ƙasar ke goyon bayan Najeriya a yaƙi da ta’addanci.

Sai dai Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, ya zargi manyan ƙasashen duniya da kawo wa Najeriya cikas wurin yaƙi da ta’addanci saboda ƙin sayar mata da makamai.

Ranar Asabar ne wasu da ake tunanin ‘yan Boko Haram ne suka yanka mutum aƙalla 43 yayin da suke tsaka da ayyuka a gonakinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *