Zulum ya jagoranci jana’izar manoma 43 da aka yi wa yankan rago a Zabarmari

Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Borno ya jagoranci jana’izar mutum 43 da Boko Haram ta yi wa yankan rago a Zabarmari da ke Ƙaramar Hukumar Mafa a jihar.

Zulum ya je garin ne da safiyar Lahadi, inda mazauna yankin suka faɗa masa cewa har yanzu ba a gama tantance yawan waɗanda aka kashe ba da kuma waɗanda suka ɓata.

Ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International ta ce akwai mata guda 10 da ba a san inda suke ba, waɗanda ke aiki a wata gonar shinkafa da ke garin na Koshebe.

Mutum 16 daga cikin waɗanda aka kashe ‘yan gudun hijira ne, in ji Amnesty.

Shugaban Muhammadu Buhari ya yi Alla-wadai da kisan a cikin wata sanarwa da kakakinsa Garba Shehu ya fitar.

A ranar Asabar ne aka samu rahotannin da ke cewa wasu da ake tunanin mayaƙan Boko Haram ne sun shiga gonaki kuma suka kashe fiye da mutum 40.

Lamarin ya faru ne a yankin Koshebe na Zabarmari da ke cikin Ƙaramar Hukumar Mafa ta Borno, kamar yadda wasu mazauna yankin suka tabbatar maharan sun abka wa manoman ne yayin da suke girbin shinkafa. Kuma bayanai sun ce an ɗaure manoman ne sannan aka yi masu yankan rago.

Wani mazaunin yankin da ya buƙaci a sakaya sunansa ya shaida wa manema labarai cewa sai da aka tara mutanen wuri guda sannan aka rinƙa yanka su har mutum 43 cikinsu har da baƙi da ke zuwa daga wasu jihohi domin su gudanar da ayyukansu a ƙauye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *