Tabar Wiwi Ta Sa An Tsinka Igiyar Aure A Jihar Oyo

Wata Kotun Al’adu da ke zama a Ibadan ta raba auren wata tela, Adija Adebayo ta mijinta, Ademola Adebayo, saboda shan wiwi da ya ke yi.

Da take bayani a gaban kotun, Adija da ke zaune a unguwar Academy da ke Ibadan, ta ce raba auren ya zama dole saboda dukan dansu mai shekara daya da rabi da Mijin ke yi da kuma lalata mata kayan aiki idan ya sha wiwi.

Ademola, wanda matukin Bas ne ya ki amince wa da raba auren, inda kuma ya ce maganar shan wiwi da ta yi kazafi ne. Ya kuma roki kotun a kan kada ta raba auren saboda yana son

Bayan sauraron bayanan su, sai Mai shari’a Ademola Odunade, ya raba auren domin a samu zaman lafiya.

Ya kuma ce hakkin kula da tarbiyar yaron yana wuyar matar, inda ya kuma umurci Ademola ya rika biyan ta Naira dubu biyar duk wata a matsayin alawus din abinci da biyan kudin makaranta da sauran dawainiyarsa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *