Iran na zargin Isra’ila da kashe mata masanin nukiliya

Shugaban Iran ya zargi Isra’ila da kisan babban ƙwararre kan shirin nukiliyarta ranar Juma’a, tana mai cewa ba za ta taɓa ja da baya ba game da shirin.

Hassan Rouhani ya kuma ce ƙasarsa za ta yi ramuwar gayya game da kisan Mohsen Fakhrizadeh a lokacin da ta zaɓa.

An kashe Fakhrizadeh ne a wani harin kwanton-ɓauna da ‘yan bindiga suka yi a kan motarsa a garin Absard da ke gabashin birnin Tehran.

Isra’ila ba ta ce komai ba game da batun zuwa yanzu, amma ta taɓa zarginsa da jagorantar wani shirin ƙera makamin nukiliya a baya.

Fakhrizadeh ne mafi shahara a cikin masana kimiyyar nukiliya na Iran, wanda ya jagoranci shirin a ƙarƙashin ma’aikatar tsaro.

Kisan nasa ka iya ƙara rura wutar rikici kan shirin ƙera nukiliya da Iran ke yi tsakaninta da Amurka da sauran ƙawayenta da suka ƙulla yarjejeniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *