Za mu gurfanar da mayakan Boko Haram-Chadi

Gwamnatin Chadi ta ce, za ta gurfanar da mayakan Boko Haram 58 a gaban kotu domin yi musu shari’a kan shiga ayyukan ta’addanci bayan sojojin kasar sun kama su a fagen-daga.

Ministan Shari’ar kasar, Djimet Arabi ya sanar da shirin gurfanar da mayakan, matakin da ke zuwa bayan kasar ta ce, ta murkushe mayakan tare da kashe sama da dubu 1 a cikinsu a zagayen Tafkin Chadi.

Gwmnatin Chadi ta gargadi cewa, sauran mayakan da sojojinta suka fatattaka sun fantsama cikin kasashen Najeriya da Nijar da ke makwabtaka da Chadin.

Shugaba Idriss Deby ya kuma gargadi kasashen Tafkin Chadi cewa, dakarunsa ba za su sake shiga yaki da Boko Haram a wata kasa ba bayan zargin kasashen da nokewa.

Ana kallon dakarun Chadi a matsayin zarata da ake alfahari da su a yankin Tafkin Chadi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *