‘Yan India sun yi jana’izar dabbar da suke bauta duk da coronavirus

A kalla mutane sama da 200 suka bijire wa dokar hana fita a India wadda aka kafa saboda hana bazuwar coronavirus, inda suka halarci jana’izar wani bijimin Sa da suke bauta masa, yayin da wasu suka yi ta rusa kuka saboda mutuwarsa. 

Wannan bijimin San mai suna Mooli ya mutu ne ranar Lahadin da ta gabata, abin da ya sa mazauna kauyen da ke jihar Tamil Nadu suka shiga alhinin rashinsa, yayin da suka yi gangami domin yi masa jana’iza.

An samu wasu mutane daga kauyuka makota da su ma suka halarci jana’izar.

Shugaban al’ummar Yankin, P. Rajasekaran ya ce, a kalla wadanda suka halarci jana’izar sun kai 200 domin yin ban-kwana da Mooli wanda ya kwashe shekaru 20 a kauyen.

Kazalika Mooli ya shahara wajen lashe kyautuka a gasar tseren dabbobi da aka dauki tsawon shekaru ana gudanarwa a jihar.

Wani jami’in Karamar Hukumar Yankin T.G. Vinay ya ce, tsakanin mutane 30 zuwa 50 suka samu jana’izar amma kuma wadanda suka zo daga baya sun kai 200, inda suka ziyararci kabarin bijimin, suna ban-kwana da shi, yayin da wasu kuma ke neman tubarruki daga wurinsa.

Wani mazaunin kauyen Kalubambarai ya ce, hatta mata sun yi ta zubar da hawaye sakamakon babban rashin da aka yi, inda yake cewa ba don dokar hana fita da aka saka a India ba, da dubban mutane ne za su halarci jana’izar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *