Trump zai fara yakin neman zabe duk da coronavirus

Shugaba Donald Trump na Amurka ya bayyana fatan ci gaba da yakin neman zabensa tun kafin shelanta kawo karshen annobar coronavirus wadda ta lakume rayukan dubban Amurkawa.

Duk da cewa a wannan yanayi abu ne mai wuya a gudanar da tarukan da za su hada dubban mutane, amma Trump ya ce, yana da niyar ficewa daga birnin Washington don gabatar da jawabi a makarantar aikin soji ta West Point da ke birnin New York ranar 23 ga watan gobe.

A ranar 3 ga watan Nuwamba mai zuwa ake sa ran gudanar da zaben shugabancin Amurka, zaben da shugaba Trump ke fatan tazarce.

Shugaban ya ce, ba ya fatan gudanar da yakin neman zabensa a yankunan da aka tsananta dokar bada tazara tsakanin al’umma don hana yaduwar cutar coronavirus, yana mai cewa, hakan zai rage wa gangaminsa armashi.

An tabbatar da mutuwar mutane fiye da dubu 36 bayan kamuwa da cutar coronavirus a Amurka.

Leave a Reply

Your email address will not be published.